Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Labarai

Maganin Corona na Kasar Madagascar baya maganin Komai– Ministan Lafiya

Gwamnatin Najeriya ta ce maganin da aka karbo daga kasar Madagascar na warkar da cutar coronavirus baya maganin Komai.

Ministan lafiya na Najeriya Osagie Ehanire, ne ya sanar da haka, inda yace cibiyar binciken magunguna ta kasar ta bayyana rahoton binciken da ta yi,akan maganin
inda ta ce maganin na Madagascar na da sinadaran da za su iya rage yawan tari ne amma ba waraka ce ga cutar Covid 19 ba.

Tun dai watan Afrilu ne shugaban kasar Madagascar Andry Rajoelina ya kaddamar da wannan maganin a matsayin maganin Corona,Wanda yace yana maganin Cutar.

Dama dai Hukumar lafiya ta duniya WHO ta yi kashedi a kan shan maganin kasar Madagascar Da ta samar ba tare da sa idon likita ba.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: