Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Labarai

Gwamnati Ta Amince za’a Rubuta Jarabawar WAEC a Najeriya

Najeriya ta sauya matsayinta na rubuta Jarabawa.
A baya gwamanatin ta hana yara masu shirin kammala karatu damar rubuta jarabawar bana,

Sai dai yanzu ta sauya sabon matsayin da ta dauka na bude makarantun sakandare daga ranar 4 ga watan gobe domin gudanar da jarabawar.

Mai magana da yawun Ma’aikatar Ilimin Najeriya Ben Goong ya ce gwamnati ta sake matsayinta wajen amincewa da shirin gudanar da jarabawar wadda za ta fara daga ranar 17 ga watan Agusta mai zuwa.

Jami’in ya ce bude makarantun ranar 4 ga watan gobe zai bai wa daliban da ke aji 3 na manyan sakandare damar shiryawa na makwanni biyu kafin fara jarabawar.

Wannan sabon matsayi ya soke wanda Ministan Ilimi Adamu Adamu ya dauka wanda ya bayyana dakatar da jarabawar na illa-masha-Allahu saboda karuwar masu kamuwa da cutar coronavirus a Najeriya.

Tun a bayan daukar wancan matsayi, ministan ilimi Adamu Adamu wanda ya ce alhakin yara daliban Najeriya na wuyarsa ne.

Acewarsa shi bai ki ba ace an soke jarabawar Africa ta Yamma gaba daya a wannan shekara domin kare lafiyar yara daga Kamuwa da Cutar Corona.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: