Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Labarai

Da gaske Ali Nuhu ya ƙara aure?

 

A ƴan kwanakinnan ake ta yaɗa wasu hotuna da ke nuni da tsarin angwancewa a zahiri wanda duniya ta ɗauka cewar ko jarumin ya ƙara aure ne.

Mutane na ta tunanin ko jarumin ya ƙara aure ne bisa wasu hotuna da ke yawo a dandalin sada zumunta.

Hotunan farko da suka fara yawo sun nuna jarumin da wata tsaleleliyar budurwa wanda ake sukai kama da hotunan nan da ake yi gab da biki.

Ba a daɗe ba kuma sai wasu hotunan suka sake ɓulla wanda aka ga tsarin biki ziryan kuma jarumin ya fito tamkar wanda aka saka a lalle

Jarumai da dama sun ta saka hotunan a dandalin sada zumunta musamman instagram, wasu ma na faɗar Allah ya sanya alheri.

Sai dai wata sanarwa da jarumi Mal. Ibrahim Sharukhan yaa fitar ya ce sam batun ba haka yake ba domin shi ya shiryaa hakan don tallata yadda suke gudanar da sana arsu ta tsara biki ga jama a.

Za ku ji mu da tattaunawarsmu da jarumi Ali Nuhu kan wannan batu.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: