Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Labaran jiha

Mun shirya tsaf don kama masu karya dokokinmu da sallah – Karota

“Batun dokar kamen goyo tana nan daram” inji Karota.

Hukumar kula da tuƙi a jihar Kano Karota ta tabbatar da cewar ba za ta bari a gudanar da wasan  guje gujen ababen hawa da sunan murnar sallah ba.

Mai magana da yawun hukumar Nabulisi Abubakar Ƙofar Naisa ne ya sanar da hakan yana mai cewar, hukumar za taa kama duk wamda aka samu ya karya dokar tuƙi yayin bikin sallah.

Haka kuma ya ce, batun dokar hana ɗaukar fasinja sama da biyu tana nan daram dam.

Sannan ya ce dakarun karota za su fito don tabbatar da cewar kowa ya bi dokar tuƙi a jihar Kano.

Kuma ya buƙaci iyaye da su guji bawa ƴanƴansu abin hawa musamman waɗand ba su kai minzalin tuƙi ba don gujewa afkuwar haɗɗura a jihar.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: