Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Labarai

Arfa – Ganduje ya shirya addu’a ta musamman kan zaman lafiya da Corona

Gwamnan jihar Kano ya shirya addu a ta musamman ne don neman yaye annobar corona virus.

Sanarwar da Babban sakataren watsa labaran gwamnan kano Mallam Abba Anwar ya fitar, ya ce, Gwamna Adullahi ganduje ya ce yana da matuƙar muhimmanci a maida hankali wajen addu a don ganin ƙarshen wannan annoba.

Malamai 360 ne suka halarci taron addu ar, kuma an yi addu a kan matsalar tsaro da ake fuskaanta aa jihohin Zamfara Katsina da sauran jihohi.

Gwamna Ganduje ya buƙaci al ummar Kano da su cigaba da bada gudunmawa wajen addu a tare da bin dokokin da masana kiwon lafiya don kare kai daga kamuwa da cutar Covid 19.

An gudanar da taron addu ar ne yau a fadar gwamnatin Kano.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: