Daga Bashir Muhammmad

A cikin hudubar da ya gabatar a yau yayin hudubar da ya gabatar a wurin Arfa Limamin masallacin harami ya bayyana cewa Manzon Allah sallahhu alaihi wassallam ya ce su gujewa Cutar kuturta kamar yadda ake gujewa zaki.
Haka kuma ya kara da cewa wannan dalilin ne yasa hukumomi a saudiya suka takaita adadin masu zuwa Aikin hajji a bana.

Kazalika Limamin ya yabawa Al’umma da basu hakuri akan jure halin da ake ciki yanzu.

Sannan yayi Kira ga Al’umma da suyi riko da amana da biyan bashi idan sun karba.
Haka kuma limamin ya bayyana cewa musulunci ya koyar da yadda zamu kaunaci yan uwanmu musulmai.
Haka kuma yayi addu’ar Allah ya taimaki shugabannin musulmai a duk inda suke.
A cikin hudubar ta sa yayi addu’ar Allah ya taimaki shugabannin saudiya bisa kula da masallatai guda biyu da suke yi.