Wata Gobara da tashi a Garin rijau dake Karamar Hukumar Rijau a Jihar Niger tayi sanadiyar Mutuwar Mata bakwai.
Gobarar dai ta tashi ne a daren jiya da misalin karfe 8:15 a shagon gyaran gashi na Afrash Beauty salon dake unguwar Bawa a Karamar Hukumar Rijau bayan Injin janareto ya kama da wuta.
Kwamishinan yan sanda na Jihar Niger ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya shaidawa Kamfanin dillancin labarai na kasa reshen Jihar Cewa Dagacin garin Rijau Alhaji Muhammmad Bello shine ya Kai Rahoton Mutuwar matan a ofishin yansandan yankin.
Rahotannin dai na nuni da cewa matan sun yi bacci ne a shagon a lokacin injin na aiki.
Sai dai Kwamishinan yan sandan yace tuni suka kwashe gawarwakin zuwa Babban asibiti dake Garin Tunga Magaji don Gudanar da bincike.
Madogara Solace base