Gwamnatin jihar Legas ta kulle makarantu 10 saboda karya dokar rufe makarantu da gwamnatin tarayya da jiha ta yi.

Darakta a ofihsin tabbatar da ingantaccen ilimi ta jihar Abiola Seriki-Ayeni ce ta tabbatar da hakan, ta ce hakan ya bbiyo bayan karya dokar rufe makaratu da gwamnatin ta bada umarni a yi.
Ta ce za a cigaba da bibiyar sauran makarantu don ganin an tabbatar sun bi dokar da aka saka.

Ta ƙara da cewa ba an rufe makarantun ne don ra’ayi ba sai don tabbatar da kare lafiyar ɗalibai a jihar.
