Wata Mata dake da ‘ya’ya uku mai suna Oluwayemisi Ajakaye ta shigar da kara a kotun majistare dake Mapo a Ibadan, tana rokon kotu ta raba auren ta da mijinta na tsawon shekaru 12.

Oluwayemisi ta kawo kukanta kotu ne saboda yadda mijinta ke cin zarafin ta a kullun
Acewarta mijin ta Segun na kiran ta da suna alade sannan har kwatanta da wasu munanan dabbobi yake yi bayan Duka da yake min.
A cewar Segun a kullum bata da natsuwa da kwanciyar hankali a gida na domin a kullum sai ta fuskanci Cin zarafi
Kazalika ko mahaifiyarta bata tsira ba domin a duk lokacin da ya yi mata waya sai ya yi barazanar kashe ta.

Oluwayemisi ta nuna wa kotun tabo da raunin dukar da ta ke sha a wajen mijinta Segun
Sai dai mijin nata Segun bai zo kotu ba duk da cewa an kai masa sammace har sau uku.

Alkalin kotun Ademola Odunade ya raba auren sannan ya bai wa Oluwayemisita rikon ‘ya’yan su uku da suka haifa tare.
Alkalin ya umurci Segun ya rika biyan naira 15,000 duk wata domin ciyar da ‘ya’yan.