Hukomomin katafaren kamfanin cinikayya a Najeriya Shoprite sun sanar da cewar za su yi ƙaura daga Najeria bayan shekaru 15.

Amfanin ya sanar da hakan ne a safiyar yau litinin.
Hukumomin kamfanin sun sanar da cewar za su bar Najeriya ne bayan gudanar da kasuwancin wucin gadi na tsawon shekaru 15 a ƙasar.

Kamfanin na da reshe a jihohin Kano, Legas da kuma babban birnin tarayya Abuja.
