Ƙungiyar kwararru ta Afrika ce takarrama gwamnanan Kano Abdullahi Umar Ganduje a matsayin wanda ya fi kowa yaƙi da annobar Corona.

cikin takardar karramawar wadda sakataren ƙungiyar Diouf Bakri Koalack ya sanyawa hannu kuma aka miƙawa gwamnan, ƙungiyar ta ce ta duba ƙoƙarin da gwamnan ke yi ne har ta zaɓoshi don zama zakaran gwajin dafi.

Takardar ta ce “ƙoƙarin da kake na ganin ka shawo kan annobar Corona ka cancanci kwaikwayo daga sauran gwamnoni.”A cewar ƙungiyar.

ƙungiyar dai ta kasance tana shuganatar ƙasashe da dama a Afrika.

ko da a baya bayan nan ma shugaban cibiyar da ke yaƙi da cutuka masu yaɗuwa a Najeriya sai da ya jininawa gwamnan a bisa irin ƙoƙarin da yake na ganin ya shawo kan annobar Corona a jihar Kano

Leave a Reply

%d bloggers like this: