Hukumar Lafiya ta duniya WHO ta yi bayyana cewa za a shafe wasu lokuta masu tsawo ba’a samu nasarar kawar da cutar coronavirus ba.

Hukumar ta WHO ta bayyana haka ne, bayan gudanar da taron gaggawa kan halin da ake ciki dangane da yakar annobar, watanni 6 bayan bullar cutar a kasar Chana tun a watan disambar shekarar 2019.
Zuwa yanzu annobar ta lakume rayukan sama da mutane dubu 680 a lokaci guda kuma yawan wadanda suka kamu da cutar a fadin duniya ya haura miliyan 17, sai dai sama da miliyan 10 daga ciki sun warke.

Hukumar lafiya ta duniyar da ta jaddada mahimmancin goyon bayan al’umma a yakin da ake da Cutar Corona.
