A wata tattaunawa da bbc suka yi da Dakta Mairo Mandara ta ce duk jariran da ake bawa madarar shanu za su taso da ɗabi un saniya.

Ta ce yana da matuƙar muhimmanci iyaye su kasance masu bawa ƴaƴansu nononsu, saɓanin na shanu da suke bayarwa.
Ta ƙara da cewa shi nonon yana gina kwakwalwar jarirai ne tun daga ranar da aka haifeshi zuwa wata shida.


Ta cigaba cewa ita kanta mai jego na ƙara samun lafoya idan tana shayar da jariri, sannan kwakwalwar jariri za ta tashi da ɗabi un mai jegon akasin haka kuwa sai su tashi da ɗabi un shanu idan aka basu nonon saniya.
“Idan ya kasance jariri ya sha nonon mahaifiyarsa zai tashi ta nutsuwa, idan kuma aka bashi nonon shanu, zai tashi da ɗabi un shanu na rashin nutsuwa da rashin kamun kai” inji Dakta.