Abdul D One mawaƙin da ake damawa da shi a masana antar fina finai ta Kannywood ya saƙi waƙa ta farko da ya fito a faifan bidoyo mai auna KECE TAWA.
Mawaƙin da ya bayyanawa Mujallar Matashiya cewar, a tsawon shekaru 10 da yayi yana waƙa bai taɓa fita a faifan bidiyo ba sai a yanzu.
Asalin sunansa Abdulƙadir Tajudden wanda aka haifeshi a garin Dikke da ke ƙaramar hukumar Funtua a jihar Katsina.
An haifeshi a ranar 26 ga watan satumba na shekarar 1994.
Ya zauna a ƙarƙashin kamfanin Shareef Studio da ke ƙarƙashin jagoranci da kulawar mawaƙi Umar M Shareef.
Duk da kasancewar mawaƙin yana garin Kaduna don cigaba da gudanar da sana arsa ta waƙa.
Waƙoƙinsa sun yi shura kuma ana sakasu a fina finai da dama, wasu kuma kan bashi aikin waƙa don su fito a cikin bidiyon.
Duk da kasancewarsa mawaƙi mai ƙaramin shekaru idan aka kwatanta da sauran manyan mawaƙa da ludayinsu ke kan dawo, Abdul D. One ya shahara wanda ya samu lambobin yabo da dama a kan waƙoƙinsa.
Ya kan yi waƙoƙin da suka danganci yanayi musamman waƙarsa ta kwananan wanda ya yi a kan rashin tsaro a Najeriya.
Ko da Mujallar Matashiya ta tambayeshi ya yaji bayan da ya saki wannan bidiyon waƙarsa ta farko a shafinsa na Youtube?
Abdul D One ya ce ya ji daɗi ga yadda aikin ya kasance kuma ya samu yabo da yawa daga mutane daban daban a kan waƙar.
Wasu daga cikin waƙoƙinsa waɗanda suka shahara akwai :-
1 Mahaifiya
2 Kar ki manta da ni
3 Dakta Bahijja
4 Abokiyar Rayuwa wanda Adam Zango ya fito shi da jaruma Zee Fretty.
5 Jaruma a cikin fim ɗin Jaruma.
6 Nawwara
7 Shaƙuwa
8 Baya ba zani
9 Waƙar biki ta gidan biki wato Ga Amarya
10 Abinda yake Raina wanda aka saka a fim ɗin mansoor