Cibiyar daƙile yaɗuwar cutuka a ƙasar Amurka ta tabbatar da cewar mutane na mutuwa wasu kuma na kamuwa da cuta bayan sun yi amfani da hannun da ke ɗauke da man kariya daga cutuwa a abincinsu ko abin sha.

Sanarwar da cibiyar ta fitar a ranar Laraba, ta ce aƙalla mutane 15 ne suka kamu da cuta bayan sun yi amfani da hannunsu a abinci.

Jaridar CNN ta rawaito cewa mutane 15 ɗin da suka kamu da cutar manya ne duk da cewar akwai ƙananan yara da wasu suka mutu wasu kuma suka kamu da cutar sanadin mfani da hannunsu da ke ɗauke da man kariya daga cuta.

Man kariya na Sanitizer na ɗauke da sinadarin Methanol wanda ya zama kamar guba ga jikin ɗan Adam.

Leave a Reply

%d bloggers like this: