Sanarwar hakan mai ɗauke da sa hannun kakakin hukumar Nabulisi Abubakar K/Naisa.

Hukumar Kula da tuƙi a jihar kano Karota ta haramta lodin manyan motoci a da rana.
Hanawar za ta fara aiki ne daga ranar 10 ga watan agustan da muke ciki.

Titunan da hukumar ta haramta lodin manyan motocin da rana sun haɗa da titin singa, ƴan kura, Igbo road, sabon gari da france road.

Hukumar ta ce daga wannan rana ta haramta lodi ko saukalen kaya na manyan motoci illa da daddare.
Sanarwar ta ce masu manyan motocin za su iya cigaba da amfani da filin idi da ke koffar wambai, da kuma filin fakin na ɗan gwauro kafin shugabannin kasuwar su gabatar da inda masu manyan motocin za su cigaba da ajiye motocinsu ba tare da sun haifar da cunkoso ba.
Hukumar ta yi gargaɗin cewar ta haramta ajiye manyan motoci a kowanne titi a jihar Kano.