Wani hadarin jirgin ruwa da aka yi a kauyen Birjingo dake Karamar Hukumar Goronyo yayi Sanadin Mutuwar Mutane 9.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan Jihar Sokoto Muhammad Sadiq ya tabbatar da faruwar lamarin.

Kamfanin Dillancin Labarai Najeriya ya rawaito cewa ya ce hadarin ya auku ranar Laraba.

yanzu haka dai rundunar yan sanda na gudanar da bincike domin gano adadin yawan mutanen dake cikin jirgin a lokacin da hadarin ya auku.

Mai rikon kwaryan shugabancin karamar hukumar Goronyo Zakari Shinaka ya ce hadarin na faruwa ya aika da mutum 50 domin ceto mutanen da jirgin ruwan ya kife da su.

Shinaka ya yi kira ga masu daukan mutane a jirgin ruwa da su daina dankara mutane fiye da yadda jirgin zai iya dauka.

Ya kuma jajantawa iyalen mutane shida da suka rasu a hadarin kuma ya umurci masu unguwanni da suka damke duk wani mai mallakin jirgin ruwan da aka dauki Mutane sama da adadin da ya kamata ya dauka.

Premiums time ta Rawaito cewa mafi yawan mutanen da ke jirgin manoma ne Kuma ‘yan kwadago dake aiki a Wani gona dake tsallaken wannan Rafi.

Photo/ premium times

Leave a Reply

%d bloggers like this: