Wasu ƴan bindiga sun hallaka Musa Mante ɗan majalisa mai wakiltar mazabar Baraza/Dass a jihar Bauchi.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Bauchi Ahmed Wakil ne ya tabbatar wa da kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN hakan.
Ahmed Wakil ya ƙara da cewa ƴan bindigar sun yi awon gaba da yaron ɗan majalisar da matansa biyu.

Wata majiya ta shaida wa NAN cewa an kashe Mista Mante ranar Alhamis a gidansa da ke Dass.

Hare haren ƴan binda ga dai na cigaba da ta azzara a yankuna daban daban na jihohin Najeriya.