Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta sake ceto wani matashi mai suna Ibrahim Lawal a unguwar Shekar Ɗan Fulani a ƙaramar hukumar Kumbotso.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar kano DSP Abdullahi Haruna ya tabbatar da cewar matashin mai shekaru 35 a duniya a tsareshi na tsawon shekaru 15 ba tare da kyakkyawar kulawa ba.

Bincike ya nuna cewar kishiyar mahaifiyar matashin bata gidan kuma tayi duk ƙoƙarinta na ganin an kuɓutar da shi.

Sai dai ana tunanin matashin na da taɓin hankali.

DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce tuni aka kai matashin asibiti don kula da lafiyarsa.

Sai dai babu rahoton samun mahaifin matashin yayin da jami an ƴan sanda suka je gidan.

Hakan na zuwa ne kwanaki uku da gano wani matashi da aka tsare shekara bakwai ba tare da kulawar abinci ko lafiya ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: