Al amarin ya faru ne a ranar litinin yayin da wasu matasa biyu ke yin faɗa a unguwar ɗan tsinke da ke ƙaramar hukumar kumbotso a Kano.

Wani mai suna Auwalu Ibrahim da ya ke zaman yayan mamacin shi ya kai ƙorafin wajen ƴan sanda kuma tuni jami an suka bazama don kamo waɗanda ke da hannu a ciki.
Sani Ibrahim mai ahekaru 23 a duniya ya rasa ransa bayan da wani Haruna Ya u ya caka masa almakashi a ƙirji kamar yadda ya amsa laifin da bakinsa a wajen ƴan sanda.

Tuni kwamishinan ƴan sandan jihar Kano Habu A. Sani ya bada umarnin mayar da ƙorafin zuwa sashen binciken kisan kai na rundunar.

Mai magana da yawun hukumar DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da cewar, za a gurfanar da duk wanda yake da hannu cikin kisan a gaban kotu da zarar sun kammala bincike.