Akwai yiwuwar dan wasan gaba na Barcelona Luis Suarez, ya koma tsohuwar kungiyarsa ta Ajax dake kasar Holland, bayan makomarsa a Barcelonan ta shiga hali na rashin tabbas, a dalilin lallasa su da kwallaye 8-2 da Bayern Munich ta yi a gasar zakarun Turai.

Tuni dai Barcelona ta sanya ‘yan wasanta da shekarunsu suka tura a kasuwa, wadanda ake kyautata zaton Suarez na cikinsu, la’akari da cewar shekara guda kawai ta rage a yarjejeniyar da ya kulla da kungiyar, kuma a yanzu haka babu batun tattaunawa don kara wa’adinta.

Bayanai sun ce Ajax ta soma shirin mikawa Suarez tayin yi mata kome bayan shafe shekaru 9 da rabuwarsu.

A shekarar 2007 Suarez ya soma haskawa Ajax, inda ya shafe shekaru 3 da rabi, tare da ci mata kwallaye 111 a wasanni 159 da ya buga mata, kafin daga bisani ya koma kungiyar kwalon kafa ta Liverpool dake ingila a 2011.

Yanzu haka kuma, Suarez ya ci wa Barcelona kwallaye 195 a wasanni 292 da ya buga mata, tun bayan soma haskawa a kungiyar daga watan Yulin 2014.

Leave a Reply

%d bloggers like this: