Kungiyar gwagwarmayar kwato wa matasa hakkokinsu A jihar kano mai Suna KUNGIYAR MATASAN JIHAR KANO ta nuna damuwa matuka kan yadda yan siyasa suka kwace ikon Raba foma fomai da gwamnatin Tarayya ta bada umarni na daukan Ma’aikata 1000 a dukkanin kananan hukumomin Najeriya.

A binciken da kungiyar ta gudanar ta hanyar tuntubar wakilan da zasu lura da raba ayyukan wato CO’ORDINATORS sun gano cewa an raba foma foman ne a hannun yan siyasa da suka hada sanatoci, yan majalisun tarayya, da na dokoki chiyamomi har da kansiloli.
A bangare guda kuma an raba wa masu. Rike da masarautun gargajiya.
Sai dai zargin da Kungiyar matasan jihar kano take an raba foma foman ga makusantan su ne ba wai masu bukatar Neman aikin ba.

Da yake jawabi ga manema labarai Shugaban kwamitin Tuntuba kan gano yadda akayi rabon fom din na kungiyar matasan jihar kano Comrade Kabiru I waziri da sakariyar sa Hajiya Aisha kabuga sun yi kira da shugaban kasa Muhammad Buhari da gwamnan kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da su binciki yadda aka gudanar da rabon foma foman kasancewar ba’ayishi ba bisa cancanta.

Kungiyar tayi kira Shugaban Majalisar Dattijai Ahmad lawal da na Wakilai Femi Gbajabiamila, Rndunar Yansanda, Hukumar ICPC da ma DSS da ma duk wasu masu fada aji a matakin gwamnatin tarayya da na jihohi dasu bincika yadda akayi kasafin wannan Neman aiki don yi matasan dake bukatar aikin.
Kungiyar ta tura takarda korafi da kuma kira kan a binciki lamarin a ofishin shugaban kasa Muhammad Buhari da gwamnan kano Dr Abdullahi Umar Ganduje, mai dauke da sa hannun Shugaban kwamitin bincike na kungiyar da Sakatariya Hajiya Aisha Kabuga.