kotun koli ta kasar Uganda ta zartar da hukuncin daurin shekaru biyar a kan Jose Filomeno dos Santos, dan tsohon shugaban kasa, bayan samunsa da laifin almundahana a lokacin da ya ke shugabantar asusun kudin rarar man fetur.

An fara gurfanar da Dos Santos, mai shekaru 42, a gaban kotu a watan Disamba bisa tuhumarsa da barnatar da dalar Amurka biliyan $1.5 a tsakanin shekarar 2013 zuwa 2018.

An kama Dos Santos, wanda ake wa lakabi da ‘Zenu’, da laifin karkatar da dalar Amurka miliyan $500 zuwa asusun wani banki a kasar Swistzerlnd
“Bayan samunsa da laifin aikata almundahana da kuma laifin amfani da iko ta haramtacciyar hanya.

kotun ta yanke ma sa hukuncin zaman gidan yari na shekara biyar,” a cewar alkalin kotun, Joao da Cruz Pitra.

Sauran wadanda aka gurfanar tare da Dos Santos, wanda su ka hada da tsohon gwamnan babban bankin kasar Angola, Valter Filipe da Silva, an yanke mu su hukuncin daurin shekaru hudu zuwa shida a gidan yari.

Kotun ta zartar da hukunci a kansu bayan samunsu da laifin almundahana, barna, safarar kudi, da amfani da iko ta haramtacciyar hanya.

Zenu ya kasance mutum na farko daga dangin tsohon shugaban kasa da aka yankewa hukuncin zaman gidan yari.

Wannan hukunci tamkar cika alkawarin da shugaban kasar Angola, Joao Lourenco, ya dauka ne na gurfanar da iyalin tsohon shugaban kasa a lokacin da ya ke yakin neman zabe a shekarar 2017.

Leave a Reply

%d bloggers like this: