Hukumar kididdig ta Najeriya ta fitar da sanarwar samun karuwar marasa aikin yi daga kashi 23.1 zuwa kashi 27.1 a watanni 6 na farkon shekarar nan.

Bayanan da hukumar ta fitar ya nuna cewa yanzu haka jihar Kano ke matsayin ta biyu a jerin jihohin da ke da yawan marasa aikin yi a Najeriya wadanda galibin shekarunsu ya fara daga 15 zuwa 60 .
Alkaluman hukumar kididdigar sun nuna cewa jihar ta Kano na da jumullar mutane miliyan 1 da dubu dari 4 da 20 galibinsu matasa ne da basu da aikin yi.

Yanzu haka dai Najeriyar na da alkaluman mutane miliyan 21 da dubu 764 da 617 wadanda basu da aiki.
