Hukumar Yaki da sha da Safarar Miyagun Kwayoyi ta NDLEA ta gano wani kwantena mai tsawon sahu arba’in shake da kwayar Tramadol da wasu haramtattun magunguna a tashar Brawal da ke Legas.

Mai magana da yawun hukumar Mr Jonah Achema ne ya sanar da hakan a ranar Laraba a birnin tarayya Abuja.

A cewar sanarwar, Shugaban NDLEA, kanal Muhammad Abdullah (mai ritaya) ya ce an gano ne bayan da yan sanda suka kama wata kwantena mai tsawon kamu arbain shake da buroshi da katon din Tramadol 40 da wasu haramtattun kwayoyin.

“Idan za ku iya tunawa yan sandan Apapa a Legas sun kama wata kwantena mai tsawon kafa 40 shake da kwayoyi da ake zargin Tramadol ne da Kodin a ranar 6 ga watan Agusta.

“An kama wannan kwantenar ne a ruwa sannan aka dauke ta aka kai tashar Apapa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: