Kwamishinan ilimin jihar Gombe, Dakta Habu Dahiru, a ranar Laraba, ya ce karin dalibai mata 7 na makarantar sakandaren GGSS Doma, sun kamu da cutar Korona.
Adadin daliban da suka kamu da cutar daga fara jarabawar ranar Litinin ya kai takwas.

A rahoton da aka fitar a baya ya nuna cewa wani dalibin jihar ya kamu da cutar kuma yana rubuta jarabawarsa daga cibiyar killace masu cutar.
Kwamishanan ilimin yayinda ya ziyarcu dalibin ya bayyana cewa ma’aikatarsa tare da hadin gwiwan kwamitin yaki da Corona ta gudanar da gwajin Korona 1100.

Yace “sun fi mayar da hankali kan daliban da suka dawo daga jihohi masu adadin cutar Korona mai yawa irin Kaduna, Kano, Yobe da Legas. Kawo yanzu dai sun gwada mutane 1,100. Daga ciki aka samu mutum daya dalibin makarantar sakandaren kimiya GSSS.”

Dama dai tun kafin a bude makarantun, gwamnatin tarayya da maaikatan lafiya da kwamitin shugaban kasa na yaki da cutar korona duk sun bayar da kaidoji da makarantun za su bi don kiyaye lafiyar dalibai da malamansu.