Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, karkashin jagorancin Kwamishinan ‘yan sanda Sanusi Buba ta yi nasara cafke, Mubarak Lawal, mai Shekaru goma sha shidda da haihuwa da Anas Ibrahim, mai shekara goma sha biyar da kuma Aliyu Mika mai shekara goma sha biyar dukkan su da ke kauyen Dutsen Dadi da ke cikin karamar hukumar Danmusa a Jihar Katsina, bisa zargin yiwa Safiya Basiru, ‘yar shekara goma sha uku fyade wanda bayan kowane daga cikin su ya yi lalata da ita suka jefa ta ruwa.

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina, SP Gambo Isah ya yi jawabi akan lamarin inda yace

sun yi wannan aika-aika ne a ranar 14/08/2020, inda suka yi wa Safiya Basiru a cikin gona, bayan kowane ya yi lalata da ita suka jefa ta wani gulbi, kuma ta rasu.

An samu gawarta a gulbin, aka kai ta asibitin garin Danmusa inda aka tabbatar da rasuwarta.

Gambo Isa ya ce a cikin bincike yan sanda, dukkansu sun amsa aikata lafin. Kuma ana cigaba da binciken.

Sai dai bayan binciken zasu gurfanar dasu a kotu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: