Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada tsohon dan kwallon kafar Najeriya Daniel Amokachi a matsayin mai taimaka masa kan harkokin wasanni.

Ministan wasannin Sunday Dare shine ya sanar da hakan ta cikin wata takarda da Sakataren Gwamnati Boss Mustapha ya sanyawa hannu.
Takardar ta bayyana amincewar shugaban kasa Muhammadu Buhari na baiwa Amokachi mukamin mataimaki na musamman akan harkokin wasanni
Daniel Amokachi na daga cikin fitattun ‘yan kwallon kafar da suka daga darajar Najeriya wajen lashe mata kofin Afirka da Olympics, yayin da ya taka leda a kungiyar Everton ta Ingila da Club Brugge ta Belgium da kuma Besiktas ta Turkiya wasa.

Sau 3 yana lashe kyauta dan wasan Afirka da yafi fice saboda kwarewar sa, yayin da ya taka rawa wajen kai Najeriya gasar cin kofin duniya na farko a Amurka da Faransa.

Tsohon dan wasan ya kuma lashe gasar cin kofin Afirka a matsayin mataimakin mai horar da Super Eagle.