Kwamintin da shugaban ƙasa ya kafa don bincikar dakataccen shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa a najeriya Ibrahim Magu ya miƙawa shugaban ƙasa Muhammdu Buhari rahoton binciken.
Wata majiya data nemi a sakaya sunanta tace . kwamitin ya bayar da shawarar cire Ibrahim Magu daga shugabancin hukumar tare da nada sabon shugaba a hukumar.
Majiyar tace dukda kwamitin bai kammala aikin binciken da yake ba amma ya samu Magu da laifi don haka ya bayar da shawarar cire shi.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya kafa kwamitin binciken bayan da ƙorafi yayi yawa a kansa.