Hukumar kashe gobara a jihar kano ta ceto mutane 12 bayan wani gini ya fado musu a unguwar rijiyar lemo a jiya juma’a.
![](https://matashiya.com/wp-content/uploads/2020/12/mn-1.jpg)
Jami’in hulda da jama’a na hukumar Sa’idu Muhammd ya tabbatar da faruwar lamarin, yayin da yace sun sami kiran waya hakan yasa suka garzaya wajen da gini ya faɗo kuma da zuwansu suka ceto mutane 12 daga ciki.
Sa’idu Muhammad ya kara da cewa cikin mutanen da suka ceto harda wani mutum mai kimanin shekaru hamsin a duniya.
![](https://matashiya.com/wp-content/uploads/2021/10/DSC_9894-scaled.jpg)
![](https://matashiya.com/wp-content/uploads/2020/02/matashiya-photo-2.jpg)