Abba Boss ya bayyana hakan ne a cikin shirin Abokin tafiya da aka sabawa gabatarwa a Mujallar Matashiya TV sau ɗaya a kowanne wata.

Shugaban rukunin gidajen gonar Nana Farms a Najeriya Muhammad Aminu Adamu wanda aka fi sani da Abba Boss ya barranta kansa da goyon bayan tsarin kulle makarantu a Najeriya.
Abba Boss ya ce babu dalilin kulle makarantun saboda cutar ta yi matuƙar sauƙi kuma Allah na kiyaye al umma ba yadda aka yi tsaammani ba.

Ya ce idan aka yi duba da sauran ƙasashe za a ga yadda cutar take ɓarna, amma a Najeriya ana samun sauƙin lamarin.

Ya ƙara da cewa, ko da aka buɗe kasuwanni da gidajen kallo, sharaɗin da gwamnati ta kafa na bin ƙa idojin wanke hannu da bada tazara lamarin sam ba a aiwatar da shi.
“Irin cunkoson da ake yi a kasuwanni amma a ce za ka ɗauki kuɗinka a banki ma sai an bi wasu ƙa idoji lamarin akwai yaudara a ciki.
Yara suna zaune ba sa zuwa makaranta suna koyon wasu ɗabi un daga yaran da basu da tarbiyya, yanzu haka za a zauna ba za a koma ba saboda cutar Corona?.
Aan yi cutuka daban daban amma ba a ɗauki mataki irin wannan ba saboda Corona sai a tsaya cak? Tunda mutuwa bata hana rayuwa ba cuta ma bai kamata ta hana rayuwa ba.” a cewar Abba Boss.
Sannan ya ce magana da yake a kan rufe makarantu ko dokar kulle, ba yana yi ne don adawa da gwamnati ba hasali ma shi ɗan jam iyyar APC ne kuma yana ganin abinda yake faɗa shi ne mafita ga al umma
Kalli cikakken shirin a nan https://youtu.be/qQ90pdh5cmc