Wasu mutane da ake zargin ‘yan bindiga ne sun yi garkuwa da sabuwar amarya tare da wata mai jego a kauyen Sutti da ke karamar hukumar Tangaza ta jihar Sokoto.

Wata majiya ta ce, an sace amaryar ne yayin da jerin tawagar motoci ke hangar kai ta gidan mijinta.
majiyar ta ce, mai jegon ita ce matar Magajin Garin Sutti kuma har gida aka bi ta aka saceta da jinjirinta a daren Alhamis.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, har yanzu ba a san yawan jama’ar da ‘yan bindigar suka sace ba a kan babbar hanyar zuwa Tangaza a ranar Laraba.

“Har zuwa ranar Juma’a da ta gabata, ba a ji komai game da su ba kuma ababen hawansu na nan wurin da aka sace su.
Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun harbi direbobin motocin sai dai daya daga cikin direbobin, ya samu sauki bayan garzaya dashi asibiti,
Yayin da Sauran duk sun mutu.