Rundunar ‘yan sandan jihar Oyo ta sake kama wani shahararren Dan Ta’adda, Sunday Shodipe.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, Gbenga Fadeyi ya tabbatar da hakan a ganawarsa da manema labarai a ranar Lahadi, 23 ga watan Agusta.
Mista Fadeyi bai bayar da cikakken bayani kan inda aka ajiye wanda ake zargin ba.

Kamun nashi na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan ya tsere daga hannun ‘yan sanda a ofishinsu na Mokola da ke Ibadan.

‘Yan sandan dai sun bazama neman Shodipe, wanda aka ce yana da hannu a kisa daban-daban da aka yi a karamar hukumar Akinyele na jihar..
Runfunar sun yi nasarar cafke Shodipe mai shekaru 19 inda sukace da zarar sun gama bincike zasu gurfanar dasu a gaban kotu.