Ministar Harkokin Agaji Da jinkai, Hajiya Sadiya Umar Faroukh, ta yaba da kokarin kafafen yada labarai, ma’aikatan agaji da hukumomin hadin gwiwa a daidai lokacin da ma’aikatar ta cika shekara daya da kafawa.

Ita dai wannan ma’aikata, Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ne ya kirkireya ta a ranar 21 ga Agusta, 2019 domin aiwatar da manufofi da ayyukan agaji, da rigakafin aukuwar bala’o’i tare da kai agajin gaggawa, sa’annan da gudanar da aikace-aikacen taimaka wa jama’a mabukata.

A cikin wata takardar sanarwa da mai agaza mata a harkar aikin yaɗa labarai Halima Oyelade ta raba, ministar ta yi la’akari da cewa “wannan shekara ce da aka yi abubuwa da dama, mai cike da kalubale da abubuwan sha’awa wadda a cikin ta Su ka koyi hanyoyin kai agaji ga jama’a da kula da bala’o’i.

amma a duk cikin ayyukan Sun maida hankalin Su wajen cika aikin da aka ba Su wanda ya kunshi kai wa jama’a sauki, hana aukuwar bala’i tare da agaza wa wadanda bala’i ya auka mawa,
Kazalika hukumar tayi kokarin fito da hanyoyin rage radadin bala’i idan ya faru, wanda hakan ya taimaka musu wajen inganta aikin su saboda nan gaba.”

A lokacin da ta ke yaba wa Shugaban Ƙasa a kan hangen nesa da ya yi na kirkiro ma’aikatar wadda ta kasance kan gaba wajen yaki da annobar korona, Hajiya Sadiya Umar Farouq ta gode masa saboda dora ta a kujerar shugabantar ma’aikatar da ya yi.

Haka kuma ta yi la’akari da cewa a cikin wannan shekara dayan, ta koyi muhimman darussa tare da samun sabuwar fahimta game da hanyoyi masu bullewa da marasa bullewa a wannan aiki.

Ta kuma jaddada yaba wa kafofin yaɗa labarai, ministar ta ce wadannan kafofi abokan tafiya ne wadanda tilas ne a haɗa korafi da su don samun nasara.

Leave a Reply

%d bloggers like this: