An samu rahoton asarar akalla dala biliyan 12 a Nijeriya, sakamakon rikicin manoma da makiyaya da ya mamaye sassa daban daban na kasar.

Daraktan kungiyar sa kai ta Mercy Corps, Ndubisi Anyanwu,ne ya sanar da hakan a ranar Talata a zantawarsa da manema labarai jim kadan bayan ganawa da jami’an gwamnati a garin Makurdi.

“a cewarsa sun yi kiyasin asarar akalla $12b a kowacce shekara sakamakon rikicin makiyaya da manoma. “Wannan wani babban al’amari ne kuma da zai iya shafar kasar baki daya,”

Anyanwu ya kara da cewa akwai bukatar a mayar da hankali kan rikici tsakanin makiyaya da manoma, yana mai cewa wannan ne ma dalilin da yasa kungiyar ta shiga cikin lamarin.

Ya yi nuni da cewa kungiyar Mercy Corps, da aka samar da ita karkashin hukumar USAID, ta mayar da hankali kan gina zaman lafiya na watanni 60 a Benue da wasu jihohin jihar.

Tun farko, shugabannin kananan hukumomi a jawabansu daban daban sun lissafa rashin aikin yi, rashin ababen more rayuwa daga cikin dalilan haddasa rikicin makiyaya da manoma.

Leave a Reply

%d bloggers like this: