Hukumar dake lura da Sufuri ta jihar kano KAROTA, Ta karbo Umarnin Kotun majistre dake zamanta a Gidan Murtala karkashin Mai shari’a Rakiya Lami Sani.

Kan Hana manyan motoci kirar Luxurious Lodi a ko ina a fadin jihar.
Hukumar ta shigar karar ne karkashin jagorancin Mutawakkil Ishaq Muhammad mashawarci a hukumar kan Al’amuran Shari’a.

Wanda yayi kira ga kotun da dakatar da hana diban fasinja a ko INA da manyan motocin suke yi.

Haka zalika KAROTA ta ba wa masu motocin umarni da su tashi daga Tashar sabon gari da su koma Tashar unguwa uku amma masu motocin suka bijirewa umarnin.
A don haka babban Daraktan Hukumar ta Karota Hon Baffa Babba Dan Agundi ya ja kunnen masu motocin da su ka bijirewa umarnin cewa duk abin ya faru da su suyi kuka da Kansu.
Baffa jace wajibi ne duk wanda zai gudanar harkoki a jihar kano da ya bi umarni da dokokin jihar don kiyayewa da zaman lafiya a fadin jihar.
Tun a baya dai anyi zargin manyan ana amfani da manyan motocin ne dake lodi a sabon gari suna ana jigilar yara kananan daga jihar kano inda ake mayar dasu jihohin kudu.
Wannan dalili yasa aka umarci manyan motocin dasu bar yankin sabon gari zuwa tashar unguwa uku.