Wani mutum mai suna Abdulhamid Muhammad dan shekaru 50, a ya mutu a sakamakon fadawa cikin rijiya.

Lamarin ya faru ne jiya Talata a kauyen Sha’iskawa da ke karamar hukumar Danbatta na jihar Kano
Mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Alhaji Saidu Mohammed ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwar da ya rabar wa manema labarai a ranar Talata a Kano.

A cewar sanarwar, lamarin ya faru ne a safiyar ranar Talata a lokacin da marigayin ya shiga rijiyar domin ya ceto tinkiya da ta fada ciki.

Mai magana da yawun hukumar ya ce, “wata mata CE ta sanar da Hukumar faruwar lamarin da misalin karfe 4:30 na Asuba ofishin kashe gobara ta garin Danbatta.”

Tun bayan faruwar lamarin bayan ciro gawar Muhammad daga rijiyar sannan aka kai shi Babban Asibitin Danbatta.”anan ne aka tabbatar da mutuwar yasa.

Hukumar ta kashe gobara ta shawarci mutane su dena jefa kansu cikin hadari, abinda ya fi dace wa shine su rika sanar da hukumar da zarar wani Abu ya faru don daukar matakin gaggawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: