Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi zargin ‘yan Jam’iyyar Democrat na shirin tafka magudi a zaben shugaban kasar da zai gudana cikin watan Nuwamba mai zuwa.

Donald Trump wanda ke wannan zargi jim kadan bayan Jam’iyyarsa ta Republican ta kammala amincewa da takararsa karo na biyu a zaben shugaban kasar na watan Nuwamba, Wanda zasu kara da Dan takarar Democrat Joe Biden.

Donald Trump ya bayyana zargin ne a wurin taron da ya gudana a Jihar North Carolina inda ya ce yana da shakku kan zaben mai zuwa.

Trump ya bukaci ‘ya’yan Jam’iyyar sa ta Republican su bude idanun su saboda abinda ya kira yunkurin ‘yan Jam’iyyar Democrat na sace zaben wajen kara yawan masu kada kuri’u ta gidan waya.

Kuri’un jin ra’ayin jama’a na nuna cewa Joe Biden ke sahun gaba wajen shirin lashe zaben, yayin da Amurkawa ke cigaba da bayyana rashin amincewarsu da rawar da Trump ke takawa musamman wajen yaki da annobar COVID-19 da kuma matsalar tattalin arziki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: