Labarai Da Dumi Duminsa

Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya goyi bayan hukuncin kisa, da aka zartarwa Mawakin nan, Wanda aka samu da lefin yin kalaman batanci ga Annabi Muhammad sallallahu Alaihi Wasallam.
Wannan jawabin na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan Jihar Abba Anwar shine ya fitar a yau.

Idan ba’a manta ba tun A makwannin baya ne wata Babbabr kotun Shari’a’r Musulunci ta yanke Hukuncin Kisa ta Hanyar Rataya ga wani mawaki mai suna Sharif mazaunin unguwar Sharifai dake jihar Kano,
sakamakon samunshi da lefin yin batanci ga fiyayyen Halitta Annabin Muhammad sallallahu Alaihi Wasallam,

Gwamnan kano Dr Abdullahi Umar Ganduje yace da zarar an kammala dukkanin abubuwan da Shari’a ta gindaya na daukaka kara zuwa kotun koli ko akasin haka zai sanya hannu Dan aiwatar da hukuncin kisan.