Daga Bashir Muhammad

Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Batcelona kuma dan Asalin kasar Brazil Ronadldinho ya kammala zaman kurkuku da yayi na tsawon wata shida.
Tun farko dai kotu a kasar Uruguai ce ta kama Ronaldinho da laifin shiga kasar da takardar jabu.

Wanda hakan yasa kotun ta yanke masa hukuncin zaman gidan kurkuku na tsawon watanni shida.

Yanzu haka dai Ronaldinho mai shkearu 40 ya koma kasarsa ta Brazil bayan kammala wa’adin sa na zaman kurkuku.
Ronadldinho ya taba lashe kambun dan wasan duniya har sau biyu a shekarar 2007 da 2008.
Ya kuma taimakawa kungiyar kwallon kafa ta barcelona wajen lashe kofuna daban daban a lokacin da ludayin sa kan dawo.