India ta kafa tarihi mafi muni a duniya na fuskantar karuwar masu kamuwa da cutar corona bayanda ma’aikatar lafiyar kasar ta bayyana gano karin mutane dubu 78 da 761 da suka kamu da cutar a rana guda.

Karin mutanen ya sanya India karya tarihin da Amurka ta kafa a baya na samun sabbin mutane dubu 77 da 638 da suka kamu da cutar corona a kwana guda, ranar 17 ga watan Yulin da ya gabata.

Yanzu haka dai India mai yawan mutane biliyan 1 da miliyan 300 ce kasa ta uku a duniya bayan Amurka da Brazil da annobar ta corona ta fi yiwa barna,
inda a yanzu yawan mutanen da suka kamu da cutar ya zarta miliyan 3 da rabi.

Yanzu haka dai, sabbin alkaluman hukumomin lafiya sun nuna cewa, yawan mutanen da suka kamu da cutar corona, ya kai miliyan 25 da dubu 29 da 250 a sassan duniya, daga cikinsu kuma dubu 842 da 915 sun rasa rayukansu.

Sai dai kawo yanzu akalla mutane miliyan 16 ne suka warke daga cutar a tsakanin kasashe kusan 200.

Leave a Reply

%d bloggers like this: