Alummar mazauna kauyen Sabon Garin Nasarawa da ke karamar hukumar Danmusa ta jihar Katsina suntarwatsa tawagar wasu yan bindiga da suka kai musu hari yankin a ranar talata.

rahotanni daga Katsina sun bayyana, cewa ‘yan bindigar masu tarin yawa a kan babura sun tunkari kauyen da misalin karfe 12:30 na ranar Talata.
Inda suka yi awon gaba da dabbobinsu, kayan abinci da abubuwa masu muhimmanci na jama’ar kauyen.
Amma kuma bayan da ‘yan bindigar suka sakankance cewa sun yi nasara, matasan sun yi jarumta inda suka zagaye gonaki tare da dazuzzukan da ke kusa.

Rahotanni sun bayyana cewa, matasan sun yi nasarar kashe daya daga cikin ‘yan bindigar tare da kwato dabbobinsu da suka sace.

Sai dai kuma, , ‘yan bindigar sun kashe daya daga cikin mazauna kauyen tare da raunata wani, wanda a halin yanzu yake gadon asbiti inda ake kula da shi.