Labaran ƙetare
Kotu zata yanke wa Jarumi Hukuncin Daurin shekaru 250 a gidan yari

kotu zata yanke wa Wani jarumi da yake yin fim din batsa hukuncin shekaru 250 a gidan yari.

Kotu ta kama jarimin da laifin yiwa mata da yawa fyade ciki kuwa harda karamar yarinya.
Jarumin mai suna Ronald Jeremy Hyatt, dama can ya jima a gidan yari, inda aka bukaci ya biya belin dala miliyan shida da rabi $6.6m.

Kazaliza kotun ta tuhumi jarumin fim din batsa, Ron Jeremy, da laifuka guda ashirin da suke da hadi da cin zarafin mata 12 da kuma yarinya karama, da aka gano tun a shekarar 2004, a cewar ofishin alkalin-alkalai na Los Angeles.

Mutumin wanda yake da shekaru 67, an kama shi da laifuka a watan Yuni da suka hada da fyade guda uku. Haka kuma ya amsa laifinsa.
A ranar Litinin ne 31 ga watan Agusta, aka sake gano wasu laifuka guda 20 da Jeremy ya aikata, inda aka bayyana cewa ya yiwa mata 13 fyade tun a shekarar 2004.
An bukaci Jeremy ya dawo kotu a cikin watan Oktoba. Idan aka same shi da duka laifukan da ake zargin shi dasu, za a yanke masa hukuncin shekaru 250 a gidan yari.
Labaran ƙetare
Ba Mu Da Niyyar Sauƙaƙa Haraji Akan Shigo Da Wasu Keɓaɓɓun Ma’adanai – Donald Trump

Shugaban ƙasar Amurka Donald Trump ya bayyana cewa, babu wata niyya ko shiri na sauƙaƙa haraji akan ma’adanan Steel da kuma Aluminium sakamakon barazanar kasuwanci da ƙasar ke fuskanta daga takwarorinta.

Tun a watan Janairu ne dai shugaba Trump ya sanya haraji ga abokan kasuwanci da kuma masu shiga da kayayyaki, ciki har da ma’adanan Steel da kuma Aluminium.
Trump ya yi hakan ne dai da niyyar juya akalar ƙara samun kuɗi, da kuma tsoron kar shirye-shiryensa su jefa ƙasar cikin mashashsharar tattalin arziki.

Donald Trump ya shaidawa manema labarai cewa, bashi da niyyar cire tsarin harajin akan wasu keɓaɓɓun abubuwa.

Inda ma ya kuma ƙarfafa tunanin ruɓanya tsarin harajin nan da 2 ga watan Afrilu, dan magance matsalar kasuwanci da kuma sauran matsalolin a ɓangaren.
Trump ya ce zuwa yanzu ƙasar ta samu biliyoyin daloli da tsarin, kuma nan da watan Afrilun za su kuma samun kuɗaɗe masu yawan gaske.
Labaran ƙetare
Harin Bom Ya Hallaka Mutane Fararen Hula 12 Tare Da Jikkata Wasu A Pakistan

Wani mummunan harin bom daga ƴan ƙunar baƙin wake ya hallaka mutane fararen hula 12 a ƙasar Pakistan, cikinsu harda ƙananan yara shida.

Lamarin dai ya auku ne a Arewa maso Yammacin ƙasar a jiya Talata, yayin da wasu mahara su biyu su ka tuƙo mota ɗauke da abin fashewar zuwa wajen jami’an tsaro da ƴan sanda.
Gagarumin harin dai ya haifar da yaɗuwar hatsaniya tare da rikito da rufin wani Masallaci da ke kusa da wajen, a daidai lokacin da mazauna yankin su ke gudanar da buɗa bakin ibadar azumin watan Ramadan.

Harin kuma dai ya shafi cunkoson hada-hadar kasuwanci a wajen, tare da jikkata wasu mutanen da kuma lalata gine-gine.

Jami’an tsaro sun samu nasarar daƙile maharan daga shiga sansanin sojojin wajen, bayan sun yi artabun musayar wuta da su tare da hallaka mutane shida daga cikinsu.
Kawo yanzu dai babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin kai harin, sai dai a ƴan kwanakin nan ƙungiyar ƴan Taliban ta Pakistan ta tsaurara tsangwama ga jami’an tsaro, musamman a yankunan da su ka yi iyaka da ƙasar Afghanistan.
Labaran ƙetare
Sabon Shugaban Ƙasar Ghana Mahama Ya Sha Alwashin Farfaɗo Da Tattalin Arziƙin Ƙasar

Sabon shugaban ƙasar Ghana John Dramani Mahama ya sha alwashin gudanar da mulki na gaskiya da adalci a ƙasar.

Mahama ya bayyana haka jiya Talata a jawabin da ya yi jim kaɗan bayan rantsar da shi.
A cewarsa zai tabbatar da inganta bangaren tattalin arzikin ƙasar

Babban mai Shari’a a kasar ne ya rantsar da shu a Black Star Square da ke Accra babban birnin ƙasar

Dubban mutane ne su ja halarta domin shaida rantsuwar.
Mahama ya mulki kasar tsakanin shekarar 2013 zuwa 2017.
Mahama ya lashe zaben da kaso 56 a ranar 9 ga watan Disamban shekarar da ta gabata.
Shugaban Najeriya kuma shugaban kungiyar ECOWAS Bola Ahmed Tinubu na daga cikin manyan baki na musamman da su ka halarta.
Haka kuma akwai sauran manyan shugabannin kasashen Afrika da s ka hakarta.
-
Labarai1 year ago
Mafi Karancin Sadaki A Najeriya Ya Koma Dubu 99,241
-
Mu shaƙata2 years ago
Kun San Ma’anar Kalmar Chiza Dani? Waƙar Da Ke Tashe A Kwanakin Nan?
-
Labaran ƙetare6 years ago
Wajibi ne duk wani namiji ya Auri mata Biyar ko a ɗaure shi a gidan yari— Sarkin Swaziland
-
Al'ada6 years ago
Fahimta ta a kan matsalar aure a ƙasar Hausa
-
Labarai6 years ago
Ba kwaya ƴan sandan kano suka kama ba, babu sinadarin maye a cikin maganin – NAFDAC
-
Addini5 years ago
Lokutan da ake saurin karɓar addu’a
-
Lafiya6 years ago
Menene Genotype ? Amfanin yinsa kafin Aure – Mujallar Matashiya
-
Mata adon gari6 years ago
Sinadarin gyaran gashi – Adon Gari