Wata mata mai shekaru 26 mai suna Rutendo Nhemachena ta mutu a yayin da ake yi mata wankan tsarki na shiga addinin Kirista a kogin Manyame dake kasar Zimbabwe.

An bayyana cewa aljanun ruwan ne suka shiga jikin Rutendo, inda ta haukace ta fada tsakiyar ruwan inda Fasto Isaac Manyemba yake yiwa maza da mata wankan tsarki ga Wanda suka shiga addinin kiristanci.
An dai ruwaito cewa mutanen dake tare da ita sun gano cewa aljannun ruwan sun jata cikin ruwan da karfin tsiya, su kuma basu yi kokarin ceto ta ba.
Fasto Manyemba ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace Nhemachena tafi karfin shi, kuma ya tabbatar aljanun ruwa ne suka shiga jikinta.

A cewar faston
“Sun roke ni, ni kuma na kai su bakin kogin da muke yiwa mutane maza da mata wankan tsarki, a lokacin ne aljanun suka shiga jikinta tare da janta cikin ruwan.
