“Ba’a neman suna a aikin jarida, anaa yinsa ne don hidinmatawa al’umma” Inji Mallam Abba Anwar.

Ƙwararren ɗan jarida kuma babban sakataren yaɗa labaran gwamnan Kano Mallam Abba Anwar ne ya bayyana haka yayin shirin Ƴar Cikin Gida da aka gabatar a Mujallar Matashiya TV.
Ya ce ya kamata ƴan jarida su kasance masu bibiyar duk wata hanya da za ta kawo cigaba ga al’umma, saɓanin son zuciya wanda ke sa a sauka daga turbar aikin.

Ya cigaba da cewa babu riba mutum yayi amfani da aikin jarida don neman suna ko burgewa, tsarin aikin bai bada damar haka ba.

“Menene amfanin ka yi abu mutane suna ganinka shashasha? Duk wani abu da zai iya kawo tashin hankali ko husuma ɗan jarida yana da damar ɓoye labarin don samar da zaman lafiya wannan shi ake kira (Self Cencorship)” inji Abba Anwar
“Abin baƙin ciki ne yadda za ka ga wasu ƴan jaridar basu da kwarewa a kan aiki, wata kafar yaɗa labaran ma ko fassara ce za ka jita gatsa-gatsa alamun babu masu horas da su a kan aiki” inji Abba Anwar.
Ya ce yana matuƙar takaicin yadda a wannan zamani da ake amfani da kafafen yaɗa labarai kowa ya zama ɗan jarida, kowa yana saka abinda yaga dama ko ya wallafa a shafinsa ba tare da ya san yadda tsarin gudanar da aikin yake ba.
Sannan ya shawarci ƴan jarida da su kasance suna koyon aikin daga kwararru don kaucewa sauka daga tsarin gudanar da aikin.
Haka kuma ya shawarci kafafen yaɗa labarai da su ke yin taron horas da ma aikatansu don koyar da su sabbin hanyoyi da dabarun aiki yadda za a tsaftaceshi ba tare da an wulaƙanta aikin ba.
Sannan ya ce “Duk abinda za ka rubuta ko ka faɗa,ka sani akwai mala’ikun da suke rubutawa”
Abba Anwar dai ya shafe shekara da shekaru yana aikin jarida, kuma ya samu kwarewa daga tsaffin ƴan jarida daga ɓangare daban-daban.
An haifeshi a jihar Kano a ƙaramar hukumar Dala kuma ya karanci fannin aikin jarida bayan ya yi karatu a makarantu tun daga firamare da sakadire da ma kwalejin share fagen shiga jami’a ta CAS.
Za ku iya kallon cikakken shirin idan kuka danna wannan rubutun na gaba ???https://youtu.be/p2HdqYgrjSI