Shahrarren dan bindigan da aka dade ana nema ruwa a jallo, Terwase Agwaza Gana, ya mika kansa ga jami’an tsaon jihar Benue.
Ya mika kansa ga kwamitin shirin afuwa a babbar filin kwallon Katsina ala dake karamar hukumar Katsina Ala a Arewacin jihar Benue a ranar Talata.
Da dadewa an sanya kudi milyan goma ga duk wanda ya bayyana inda Gana yake boye a jihar amma ba’a samu wanda ya iya cin kudin ba.
Wannan shine karo na biyu da zai mika kansa ga hukumar bayan ajiye makamai da harsasai ga mambobin kwamitin afuwa da gwamnan Jihar, Samuel Ortom, ya shirya.
Sai dai daga baya yayi hannun riga da gwamnatin Samuel Ortom lokacin da yake jam’iyyar APC bayan sabanin da suka samu.
Gana, wanda ake zargi da laifin kisan hadimin gwamna Ortom kan lamuran tsaro, Denen Igbana.
Ana kyautata zaton cewa shine ummul haba’isin ayyukan yan bindiga a yankin Sankera da Ukun, Logo da karamar hukumar Katsina Ala.
A yanzu haka, an garzaya da Gana gidan gwamnatin jihar dake Makurdi inda gwamna Ortom ya karbeshi.