Connect with us

Labarai

Halin da ake ciki a yanzu kowa zai iya samawa kansa mafita – Abubakar

Published

on

Gurɓacewar shugabanni! tsadar rayuwa!! Ƙunci, firgici, tashin hankali!!!
Da sunan Allah mai rahma mai jin ƙai, Allah ya ƙarawa annabi daraja.
Babu shakka waɗannan abubuwa da na fara wallafawa a sama kusan duk wani abu da zai biyo baya zai hau ƙarƙashinsu ne,haƙiƙa mutane na cikin wani hali da aka gaza gano bakin zaren.
Da yawan mutane idan ka nemi jin ra’ayinsu dangane da halin da aka tsinki kai a yau, za ka ji kai tsaye sun alaƙanta hakan ga shugabanni.
Da yawan al’amura su kan faru sai dai komai na da sababi wanda sai an bi sababin don warware yanayin da ake ciki.
Jihohi da dama ba sa cikin nutsuwa mutanen da ke rayuwa a ciki wajibi ka tausaya, ko dai ya kasance rai da lafiya bai tsira ba, ko kuma ka riski ƙuncin rayuwar da ake tamkar ba sa ƙarƙashin shugabancin ƙasar da ta mallaki arziƙi a cikinta.
Haka abin yake cigaba a kowanne lokaci za ka riski mafitar da mutane ake kamawa tamkar kumfar kogi.
Idan za mu kwatanta adalci, mu ɗauki rayuwar da ake gudanarwa a tsakani tun daga ƙasa kafin mu kalli waɗanda ke sama za mu ga cewar yanayin gurɓatacciyar raayuwar da ake gudanarwa a tsakanin mutanen da ake jagoranta a wasu lokutan ya fi ƙazanta a kan masu jagoranci.
Ga masu bibiyar kafafen yaɗa labrai sun san yadda ake kawo labaran abubuwan da ke faruwa a tsakanin talakawa a kowacce rana, wasu abubuwan ma baki ba zai iya faɗa ba.
Duk da irin yanayin da muke jefa kanmu amma muke hangen waɗanda bamusan yaya suke gudanar da rayuwarsu ba kasancewar suna inda wani ma ko hoton wajen bai taɓa gani ba.
Ta yaya za mu ga daidai? Ta yaya rayuwarmu za ta kyautata? Ta yaya al’umma za su fita daga halin da suke ciki?
Idan na shiga gonar malamai za mu ga cewar, Addinin musulunci ya tanadi hanyoyin da mutum zai samarwa kansa waraka a duk lokacin da ya so, tunda har Allah ya kan yafewa bayinsa irin kura kuren da suke yi idan suka yi tuba na gaskiya to babu shakka rayuwa za ta inganta a ji daɗinta fiye da yadda ake tsammani.
Misali, duk irin ƙuncin da ake ciki a rayuwa, mutanen da suka kasance masu ƙarancin saɓon Allah ba sa tagayyara ko jin ɗar a ransu a duk irin tsananin da za a shiga.
“Allah ya ce ku tunani a lokacin da kuka samu ni ima ni kuma zan tunaku a lokacin da kuke bukatar taimako na” Allah ya sa na faɗa daidai, da za ku kalli rayuwar mutanen da suke tunawa da Allah koda da kwayar zarra ne a yayin da suke aikata wani abu na kuskure ko ganganci, ba daidai yake da rayuwar mutanen da idanunsu ya rufe wajen saɓawa ugangiji ba tare da kawoshi a zuciya ba, wannan misali ne da za ka iya aunawa da mizanin wanda kake tare da shi.
Mu ɗauki lokaci, da za kuji ana cewa lokaci yana da albarka amma yanzu babu daɗewa nan da nan lokaci ya tafi, to mu sani cewa,albarkar lokaci tana nan kamar yadda Allah ya halicci lokaci, idan kana so ka gane, da za ka tashi cikin dare don bautawa Allah, sai ka ji kayi ka yi ka gaji daren bai ƙare ba,haka da rana, da za ka ware wani lokaci da za ka bautawa Allah cikin nutsuwa, da za ka fahimci cewa lokacin ma kamar ya maka yawa, don sai ka gudanar da duk wani abu da kake son yi kuma lokacin bai ƙure ba.
Abinda nake so mu fahimta a nan shine, kar ka damu da sai kowa ya gyaru, fara gyara kanka sai ka ƙauracewa, yunwa, tashin hankali, fargaba,firgici, da tsoro.
Waɗanda kuwa za su yi rayuwa ba tare da lisaafi ba, ma aunin a bayyane yake.
Zagi ko cin zarafin shugaba ba zai haifar da komai ba, idan ka mutu Allah zai tambayeka yaya ka yi rayuwa me da me ka aikata,kowa tambayarsa daban.
Allah ya sa mu gane mu gyara.
©️ #AbubakarMurtalaIbrahim
9/9/2020

Click to comment

Leave a Reply

Labarai

Zagon Kasan Da Kwankwaso Ya Yi Wa Jam’iyyar NNPP Ya Sa Ba Muyi Nasara A Kotuba- Alhaji Abbas

Published

on

Babban jigo a jam’iyyar NNPP, Alhaji Abbas Onilewura ya zargi dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar, Rabiu Kwankwaso kan rasa nasarar jam’iyyar a jihar Kano.

 

A jiya Laraba 20 ga watan Satumba kotun ta yanke hukunci inda ta tsige Gwamna Abba Kabir na jam’iyyar a matsayin gwamna.

 

Kotun kuma ta tabbatar da Nasiru Gawuna na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben.

 

Yayin da ya ke martani kan hukuncin, Abbas ya ce Kwankwaso ya siyar da jam’iyyar lokacin da ya ke tattaunawa da APC kan mukamin minista a Abuja.

 

Onilewura ya bayyana haka ne a yau Alhamis 21 ga watan Satumba a cikin wata sanarwa da ya fitar.

 

Ya ce zagon kasa da Kwankwaso ya yi wa jam’iyyar ce ya jawo rashin nasararta a hukuncin kotun da aka yanke a jiya.

 

Ya kara da cewa Wannan rashin nasara babbar asara ce a jam’iyyar mu kuma hakan ya faru ne saboda son rai na Kwankwaso wanda ya siyar da jam’iyyar.

Continue Reading

Labarai

Gwamnatin Delta Ta Amince Da Rage Kaso 25 Na Kudin Jami’a A Jihar

Published

on

Gwamnatin jihar Delta ta amince da rage kashi 25 na kudin makarantar daliban jami’a a jihar.

Wannan dai wani bangare ne na tallafin da gwamnatin za ta bai wa daliban kuma ya shafi jami’a hudu mallakin jihar.

Hakan na kunshe a wata sanarwa da babban sakataren yada labaran gwamnan Festus Ahon ya sanyawa hannu ranar Laraba.

Sanarwar ta ce gwamnan ya bayar da umarnin bai wa ma’aikatan jihar tallafin naira dubu goma kowanne tsawon watanni uku.

Sannan an amince da kashe naira biliyan 5.522 ga ma’aikata 50,196 a matsayinalawus da aka yi musu karin matsayi.

Sannan gwamnatin za ta kashe naira biliyan goma wajen raba buhun shinkafa 17,000 da sama da buhu masara 60,000 ga marasa karfi.

Continue Reading

Labarai

Cibiyar Kare Hakkin Yan Jaridu Ta Yi Allah-Wadai Da Cin Zarafin Yan Jarida A Kano

Published

on

Cibiyar kare hakkin yan jarida ta duniya ta yi Alla wadai da cin zarafin yan jarida da wasu yan sanda su ka yi a Kano yau Laraba.

Salim Umar na jaridar Daily Trust da Zahradden Lawal na jaridar BBC an ci zarafinsu tare da lalata layan aikinsu yayin da us ke bakin aiki.

Babban jami’in kare hakkin yan jarida na duniya Melody Akunjiyan ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya aikewa manema labarai a yau.

Cibiyar ta ce abin takaici ne ganin yadda yan sandan su ka nuna rashin kwarewa ta hanyar cin zarafin yan jaridan yayin da su ke bakin aiki.

Cibiyar ta bukaci hukumar yan sanda ta kasa da su kula tare da kiyayewa a gaba wajen cin zarafin yan jarida musamman idan aiki ya hadasu da jami’an yan sanda.

Haka kuma cibiyar ta bukaci da aka ci gaba da bai wa yan sanda horo yadda za su dinga mu’amala da yan jarida tare da mutunta darajar dan adam.

Continue Reading

Talla

Trending

%d bloggers like this: