Wata kotu da ke zama a Gabashin Pakistan, garin Lahore ta yankewa wani Kirista hukuncin kisa saboda aikata laifin batanci ga manzon Allah.

Da ya ke jawabin kare kansa a gaban kotun, Pervaiz ya yi ikirarin cewa mai gidansa ne yake matsa masa a wajen aiki akan ya shiga Addinin Musulunci.
Doka mai tsauri ta Pakistan ta haramta batanci ta sanya hukuncin kisa ga wanda ya yi batanci ga Annabi Muhammad (SAW)
Hakan na cikin matakan da Pakistan ta dauka kan cin zarafi ko batanci ga addinai, musamman marasa karfi.

Asif Pervaiz, (37) ya kasance a kulle tun 2013 a lokacin da aka zarge sa da tura sakonnin batanci ga shugabansa a wajen aiki,

Kamar yadda lauyansa Saif-Ul-Malook ya shaidawa gidan Talabijin na Al Jazeera.
Kotun ta yi watsi da bayanan da ya gabatar na karyata dukkanin zarge zargen da ake yi masa, kuma kotun ta yanke masa hukuncin kisa a ranar Talata.