hukumar kayyade farashin man fetir na tarayya PPRA ta ce daga yanzu babu ruwanta da maganar tsayar da farashin mai, magana ta koma hannun ‘yan kasuwa.

babban sakataren hukumar PPRA, Abdulkadir Saidu, ne ya sanar da hakan a jiya.
, Saidu ya bayyana cewa daga yanzu kayyade farashin litar mai zai dogara ne a kan bukatarsa da kuma farashin danyen mai a kasuwar duniya.

Hakan na nufin gwamnati ta tsame hannunta daga tsayarwa ko kayyade farashin litar mai.

Saidu, wanda babban manaja a PPRA, Victor Shidok, ya wakilta, ya ce PPRA za ta cigaba da sa-ido a kan yadda ‘yan kasuwa ke sayar da man fetur domin tabbatar da cewa ba a zalunci jama’a ba.
“Acewarsa Alhakinmu su ne su tabbatar da cewa sun kare hakkin jama’ar da ke sayen man fetur domin amfaninsu.
har yanzu ‘yan kasuwa basu fara shigo da tattaccen man fetur ba saboda karancin kudaden kasashen waje a kasuwar canjin kudade.
A makon jiya ne dai gwamnatin tarayya ta sanar da kara farashin litar man fetur, lamarin da ya sanya ‘yan najeriya shiga yanayin damuwa.