Kungiyar likitoci masu neman kwarewa ta cimma matsaya da gwamnatin tarayyaa kan yajin aikin da takeyi.

Yayin wani taro da Suka gudanar da ya dauki tsawon lokaci inda suka tsaida matsaya akan cewe sun dakatar da yajin aikin da sukeyu a yau Alhamis.
Ƙungiyar ta bayyana cewa wasu daga cikin batutuwan da kungiyarsu tasa a gaba sun hadar da samar da inshorar rayuwa ga likitoci da Kuma sake yin nazari ga kudaden da aka ware domin shiga ayyukan hadari da aka baiwa ma’aikatan lafiya.

Sai alawus din da aka baiwa ma’aikatan akan cutar Corona.

A baya can ministan lafiya Mr usaji khendare ya bukaci shugabannin manyan assibitocin gwamnati dasu maye gurbin likitocin masu neman kwarewar da lilitoci masu hidimtawa kasa da Kuma manyan likitoci domin maye gurbin likitocin da Suka tafi yajin aikin.